Rana ta take gari kuma yayi tsit, sai karar iskar bazara
na tayar da kura. Na Audu na zaune a gefen hanya yana sake-sake a ransa
dangane da kuncin rayuwa. Cikin lokaci kankani sai gashi ya tsunduma
kogin tunani yana tarawa yana debewa. A wannan yanayi ya fada tunanin
halin da yake ciki da kuma sanadin halin da alumma ta tsinci kanta. Ganin mai ruwa na tafiya sai
ya tuna masa da zancen bayaushe na ina ruwa na idan yana ganin abu bai
shafe shi. Kamar maganar wai idan jifa ya wuce ka to ya fada kan kowa!
Me za ka rasa idan ka hana jifan daga faruwa ko kuma idan ya wuce to ka taimaka kar ya fada kan kowa don ka da ya yi illa? Me yasa baza ace idan jifa ya wuce ka, ka
taimaka don kar ya cutar da kowa ba? Na Audu na ganin haka ya dace to
kana zargin wannan karin maganar akan halin da alumna ke ciki kenan?
Tambayar da Hadi yayiwa Na Audu kenan. Na Audu ya gyada kai ya kada
baki yace, a'a. Amma ina ganin idan mutum ya tarbiyantu da kalamai na
taimako zai yi amfani wajen yadda zai bullowa alamura. Halin ko in kula
da ya kawo mu cikin damuwa nake taajibi. Yanzu kaga a garin mu sai ka
bada kudi kafin kayi bacci da sauran alamura na rayuwa! Kamar yaya, bari
na Baka labari ko na fede biri har wutsiya.
No comments:
Post a Comment