1: Yau da Gobe ....
Yan uwa fa tare,
Duk da uwa da uba fa tare
Muna ta shewa fa lale
Komai fa abin dadi
Kwatsam mai faruwa ta faru
Me yanke kwauna
Mutuwa ta zo ba jinkirtawa
Wannan rana tayi daci
Rai duk yayi kunci
Wannan rana ba dogon furuci
Wannan rana mun fa zaunu
Kurum sai halartowa a zuci
Lamura da suka auku
Baza mu sake dawo wa ba
Ranar da bango ya fadi
Sai girma ya karu
Nauyi kuma ba misaltu
Son rai kuma ya kare
Sai dai kuma kyautatawa
Wanna lokacin can
Da muke ta morewa
Ban san wahalar samu ba
Ban san dadin wadata ba
Ban san dadi rashi ba, Don nayi godiya
Wannan lokaci sai yawan kokawa
Ashe duniya rawar yan mata
Ranar da na gaba ya gusa
Sai gashi na baya yau shine a gaba
Ashe dai dan adam akwai rauni
To ya kai mai sauraro
A wana hali kake fa yanzu
Idan rana tana gushewa
Wataran Kai ma ka nan
To sai muyi azama mu daure, don jin dadin likacin
Me rubuta wake /me waken nan ya fa gamsu
Rayuwa na da dadi
Idan ka kyautata
Me rage banda azama
Abun dai kamar wasa /almara
Yara sun koma manya
Ga mata kuma ga yara
Gida ya kammalawa
Duniya fa a tafe take
Haka nan lamura ke sauyawa
Sai me lura ya gane
Duniya bata waigowa
2: Matasan social media ...
Matasa ginshikin alumma
Manyan mu fa gobe
Kune masu garin fa
Matasan mu abin alfahari
Da can fa a dauri
Matasa sai yake yake
Kare kasa don ginin alumna
Noma da kiwo shine abin yi
Sun hinmatu don kyautatawa
Zamani yana ta sauyawa
Duniya tayi sauki
Yaki yana ragewa
Fatauci ya fa karu
Matasa na ta taimakawa
Ilimi ya fa karu
Kullum sai fadadawa
Matasa na ta koyo
Abin dadi da morewa
Kunga fa social media
Matasa ne suka kera
Sukai amfani da kwakwale
Ba dare ko rana , yanzu suna ta morewa
Ita wanna social media
Ta na da amfani infa kun lura
Haka ma dai da illoli
Don haka sai ku lura
Kun ga fa social media
Zai kai zumunci ka amfanu
Ga kasuwanci don mun karu
Sannan har ma da nishadantarwa
Haka ma illolin ta
Suna ta nakasa mana matasa
Kwakwale suna ta zaune
Matasa sai ku motsa su
Sai mu rage lokacin brawsing
Ko kuma social media chatting
Ko kuma kallo mara amfanu
Duk don mu kyautata gobe
Yada zancen karya
Karairari da zancen banza
Jita jita da karya
Wannan sai mu daina
Ga kalubale ga matasa
Kowa sai ya himmatu
Domin ya kyautata gobe
Har ma sai muyi masa biki
Matasan mu masu kwazo
Ga hankali da tunani
Basira har ma da wayo
Sai ku himmatu don kyautatawa
3. My small world
In progress ............
...................................
........................................
4. The long-awaited answer
In progress ............
...................................
........................................
No comments:
Post a Comment